Kun san 'yan wasan da ke daf da sauya kulob?

Yayin da kasuwar saye da sayar da 'yan wasa kwallon kafa a nahiyar Turai take ci gaba da ci, mun waiwayi wasu 'yan wasa biyar da ake ganin suna daf da sauya kungiyoyinsu.

1. Alvaro Morata

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Morata ya taba koma Juventus a shekarar 2014 kafin ya sake dawowa Madrid

Akwai jita-jitar da ke cewa dan wasan gaban Real Madrid Alvaro Morata yana shirin komawa kulob din Chelsea.

2. Alexis Sanchez

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sanchez ya koma Arsenal ne daga Barcelona a shekarar 2014

Game da batun Alexis Sanchez na Arsenal, ana daganta ta shi ne da komawa Manchester City ko kuma Bayern Munich.

Ko da yake Sanchez yana da sauran shekara daya a Arsenal, akwai rahotannin da ke cewa yana son barin kulob din.

3. Andrea Belotti

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Belotti mai shekara 23 ya koma Torina daga kulob din Palermo a shekarar 2015

Ana baza jita-jitar cewa Belotti na son komawa kulob din Chelsea ko kuma AC Milan ne.

Har ila yau, akwai rahotannin da ke cewa Chelsea ta raba kafa ne tsakanin Morata da shi - amma hakan ba yana nufin cewa za ta sayi wanda ya fi arha ne a tsakaninsu ba.

4. Kylian Mbappe

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mbappe dan shekara 18 ya fara takawa Monaco leda ne a shekarar 2015

A Spain, akwai jita-jitar da ke cewa Real Madrid tana zawarcin dan wasan gaban kulob din Monaco, Kylian Mbappe.

A farkon kakar bana, an yi tsammanin dan wasan zai koma Arsenal ne ko kuma Liverpool.

5. Naby Keita

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Keita ya koma kungiyar RB Leipzig ta kasar Jamus ce a bara

Shi kuma dan wasa Naby Keita na kulob din RB Leipzig ana alakanta shi ne da koma kulob din Liverpool.

Sai dai akwai alamun da ke nuna cewa RB Leipzig ba ta son rabuwa da dan wasan mai shekara 24.

Kun san kulob din da ya fi fice a Turai?

Labarai masu alaka