Ba za mu yi kasadar neman Ronaldo ba – Mourinho

Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ronaldo ya koma Madrid ne a shekarar 2009 daga Man U

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce ba sa neman Cristiano Ronaldo ya dawo kulob din daga Real Madrid.

A watan Yuni ne BBC ta ruwaito cewa dan wasan yana son barin Spain saboda zargin da ake masa na zambar haraji.

A baya ana ganin kamar akwai yiwuwar ya koma United wadda ya bari a shekarar 2009, inda ya koma Madrid a kan fam miliyan 80.

Yayin da aka tambayi Mourinho game da ko suna zawarcin dan wasan ne, kocin ya ce hakan ba abu ne mai yiwuwa ba, saboda "matsanancin kudin" da za a tanada wajen cinikayyar.

Mourinho ya bayyana hakan ne jim kadan bayan Man U ta doke LA Galaxy da ci 5 - 2 a wasan da suka buga a Amurka ranar Asabar.

"Ba zan sa kulob dina ya bata lokaci kan 'yan wasan da kasada ne cinikinsu,"in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: "Ronaldo babban dan wasa ne a kungiyarsa. Dan wasa ne mai tsada sosai. Ba mu da wani dalili da muke ganin cewa Ronaldo yana tunanin barin Madrid. "

Hakazalika, kocin ya ce ba sa zawarcin dan wasan Madrid Alvaro Morata wanda ake baza jita-jitar zai koma Man U.