Roger Federer ya lashe kofin Wimbledon na 2017

Asalin hoton, Getty Images
Federer ya doke Cilic da ci 6-3 6-1 6-4
Dan wasan tennis Roger Federer ya lashe kofin Wimbledon na bana bayan ya doke Marin Cilic.
Ya doke Cilic ne da ci 6-3 6-1 6-4, wanda rabon da ya lashe kofin tun a shekarar 2012.
Federer mai shekara 35 ya kafa tarihi na zama dan wasan tennis na farko a duniya da ya lashe kofin sau takwas.
Har ila yau, Federer wanda dan kasar Switzerland ne kuma shi ne dan wasa ma fi shekaru da ya lashe gasar Wimbledon tun bayan da aka sauya mata suna zuwa Open.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, MINTI ƊAYA DA BBC NA YAMMA 21/01/2021, Tsawon lokaci 1,01
MINTI ƊAYA DA BBC NA YAMMA 21/01/2021