Arsenal na tsoron kasa sayen Thomas Lemar daga Monaco

Thomas Lemar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lemar ya taimaka wa Monaco lashe gasar to the Ligue 1 a kakar bara

Arsenal ta yi imanin cewar za ta iya rasa wani muhimmin dan wasan da ta ke so, Thomas Lemar daga Monaco.

Har yanzu dai Gunners na kokarin sayan dan asalin Faransan mai shekara 21, amman ta yiwu zakarun Faransan ba sa son kyale wani dan wasa ya sake barinsu.

Ficewar Tiemoue Bakayoko zuwa Chelsea daga Monaco da kuma yiwuwar ficewar Benjamin Mendy daga Monaco na nufin cewar zai yi wuya a bari wani dan wasa ya kulla wata yarjejeniya.

Har wa yau, Arsenal na kokarin rike dan wasanta Alexis Sanchez.

Dan wasan dan asalin kasar Chile ya shiga shekara ta karshe a yarjejeniyarsa da kungiyar, kuma rahotanni na cewar yana shaukin barin kungiyar, amman Gunners na son su rike dan wasan da ya fi cin kwallaye a kakar bara.

Monaco ta sayar wa Chelsea dan wasan tsakiya Bakayoko kan wata yarjejeniyar da aka ce ta kai Fam miliyan 40, daidai lokacin da aka alakanta dan wasan baya na hagu da tafiya Manchester City.

Ana kuma rade-radin a kan cewar dan wasan kulob din Ligue 1 mai shekara 18, Kylian Mbappe, wanda Arsenal da Real Madrid ke hako shi ma zai bar Monacon.

Kawo yanzu dai 'yan wasan da Arsenal ta saya a lokacin bazara su ne dan wasan gaban Faransa Alexandre Lacazette daga Lyon kan kudi fam Miliyan 46.5 da kuma dan wasan baya na hagu Seda Kolasinac daga Schalke.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba