Sojojin Kamaru 34 sun nutse a ruwa

Kamaru Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dakarun Kamaru na yakar kungiyar Boko Haram a arewacin kasar

A jamhuriyyar Kamaru, masu aikin ceto na ci gaba da yunkurin gano wasu sojojin kasar 34 da suka bace bayan jirgin ruwan da suke ciki ya kife a gabar ruwan kasar.

Minista tsaro kasar ya ce an samu ceto wasu sojoji uku daga cikin 37 da lamarin ya rutsa da su, yayin da ake ci gaba da neman sauran.

Kawo yanzu ba a gano abin da ya haddasa hadarin ba.

Wasu rahotanni na cewa lamarin ya rutsa ne da sojojin runduna ta musamman wadda ke yaki da Boko Haram a yankin arewacin kasar.

A ranar Lahadi ne jirgin ruwan da ke dauke da jami'an tsaro 37 tare da wasu kayayyakin aiki ya tashi daga birnin Limbe ya nufi Bakassi.

Bayan sa'a guda kuma aka daina jin duriyarsa.

Karanta karin bayani kan wannan da ma sauran labarai

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce Kamaru ta tura dubban sojojinta yankin Arewa Mai Nisa domin kakkabe 'yan tada kayar bayan Boko Haram wanda suka kashe fiye da mutum 20,000 a yankin tafkin Chadi tare da raba fiye da mutum miliyan 2.7 da gidajensu.

Kungiyar na ci gaba da kai hare-hare a kasar, kuma wani harin kunar bakin waken da wasu yara suka kai kasar a watan jiya ya kashe mutum tara.

Labarai masu alaka