Nigeria: Bama-bamai sun kashe mutum takwas a masallaci

Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar Boko Haram ta saba kai hare-hare ciki da wajen birnin na Maiduguri

Hukumomi a Najeriya sun ce wata 'yar kunar-bakin-wake ta tarwatsa kanta a wani masallaci a birnin Maiduguri, inda ta kashe mutum takwas.

Wasu mutum 15 kuma sun jikkata a harin, wanda aka kai a lokacin sallar Asuba a safiyar Litinin.

Wasu rahotanni sun ce jami'an tsaro na bin 'yar kunar bakin waken da ke kokarin tserewa ne a lokacin da ta tayar da bam din da ke jikinta.

A wani lamarin na daban, 'yan sanda a jihar ta Borno dai sun yi bayyana cewa Boko Haram ta tilastawa wani yaro makiyayi dan shekara 10 yin damara da bama-bamai, kuma sun tashi a yayin da yaron ya nemi a cire masa damarar bayan ya isa gida.

Bam din ya kashe yaron tare da raunata kaninsa.

Wasu na fargabar wannan wani sabon salo ne na hare-haren da kungiyar, wacce ta dade tana fafutika, ta bullo da shi.

Karanta karin bayani game da wannan da ma sauran labarai

Wannan hari na zuwa ne a dai-dai lokacin da wani rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a watan Afrilu ya bayyana cewa an samu karuwar amfani da kananan yara wajen kai hare-haren kunar bakin wake a kasashen Najeriya da Kamaru da Chadi da kuma Nijar.

Rahoton ya kuma ce an yi amfani da yara 27 akasarinsu mata cikin wata uku na farkon wannan shekarar, idan aka kwatanta da yara 30 da aka yi amfani da su a shekarar da ta gabata.

Wasu masana a fannin tsaro a Najeriyar na kallon matsalar hare-haren kunar bakin wake a matsayin wani babban kalubale da kawo yanzu jami'an tsaro suka gaza magancewa.

Sai dai ana su bangaren jami'an tsaron na cewa suna iya kokarinsu.

Labarai masu alaka