Ramos da Marcelo sun ci kofi 15 a Madrid

Marcelo da Ramos Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan wasan biyu sun ci kofi 15 a Real Madrid

Kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos da Marcelo sun lashe kofi 15 kowannensu a kungiyar.

'Yan wasan biyu sun ci kofin Zakarun Turai uku da na Zakarun nahiyoyi biyu da La Liga hudu da Copa del Rey biyu da Uefa Super Cup biyu da na Spanish Super cup biyu.

A kakar wasannin da aka kare Ramos da Marcelo suka lashe kofin La Liga da na Zakarun Turai.

Wasu 'yan kwallon Madrid biyu da suke biye a yawan cin kofi a kungiyar su ne Karim Benzema da Cristiano Ronaldo wadanda kowannensu ya lashe guda 12.

Labarai masu alaka