Barcelona ta je Amurka da 'yan wasa 26

Kai tsake Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona za ta yi wasannin atisaye a Amurka

Sabon kociyan Barcelona, Ernesto Valverde ya bayyana 'yan wasa 26 da ya tafi da su Amurka a ranar Laraba, domin buga atisayen tunkarar kakar bana.

Dukkan 'yan wasan da suka yi atisaye a kungiyar bayan da ta dawo hutu za su je Amurkan, in banda Rafinha da Gerrard Deulofeu wadanda suke jinya.

Barcelona za ta buga gasar International Champions Cup, inda za ta kara da Juventus ranar 22 da watan Yuli da Manchester United 26 ga watan da kuma Real Madrid a ranar 29 ga watan na Yuli.

Ga jerin 'yan wasan Barca da ta je da su Amurkan:

Pique da Rakitic da Sergio da Denis Suarez da Arda da Iniesta da Suarez da Messi da Neymar Jr. da Cillessen da Mascherano da Paco Alcacer da Jordi Alba da Digne da S. Roberto da Aleix Vidal da Umtiti da Semedo da Marlon da Douglas da Samper da Vermaelen da Munir da Ortola da Jokin da Ezkieta da kuma Alena.

Labarai masu alaka