Szczesny ya kammala komawa Juventus

Kai tsaye Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan wasan ya taka rawar gani a Roma

Mai tsaron ragar Arsenal, Wojciech Szczesny ya kammala komawa Juventus kan kudi fan miliyan 10 kan yarjejeniyar shekara hudu.

Golan mai shekara 27, ya buga wasa aro kaka biyu a kungiyar kwallon kafa ta Roma daga Arsenal.

Szczesny ya yi wa Roma wasa 38 a kakar da ta kare, inda ya buga wasa 14 kwallo bai shiga ragarsa ba, wanda hakan ya sa yayi gwaninta a gasar Serie A.

Mai tsaron ragar zai zama mai taimakawa Gianluigi Buffon a Juventus wadda ta lashe kofin Serie A da aka kammala kuma na shida a jere.

Labarai masu alaka