Aguero ba zai bar Man City ba — Guardiola

Aguero Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Aguero zai ci gaba da taka-leda a Ettihad

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya ce Sergio Aguero ba zai bar Manchester City a kakar bana ba.

An yi ta alakanta cewar Aguero mai shekara 29 wanda ya ci kwallo 122 a gasar cin kofin Premier zai koma Chelsea da murza-leda.

An ce kocin Chelsea, Antonio Conte na son daukar Aguero domin ya maye gurbin Diego Costa wanda ya ce ba zai yi amfani da shi a wasannin kakar da za a fara ba.

Aguero ya ci kwallo 20 a gasar Premier da ta kare, sai dai kuma Gabriel Jesus ya maye gurbinsa a watan Fabrairu, inda hakan ya sa ake cewa zai bar Ettihad.

Labarai masu alaka