Chelsea ta amince ta dauki Morata

Morata Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyoyi da dama sun nemi Morata a bana

Chelsea ta amince ta dauki dan wasan Spaniya, Alvaro Morata daga Real Madrid, idan dan kwallon ya amince da yarjejeniyar da aka yi masa tayi, sannan likitoci su gwada lafiyarsa.

Morata ya koma Madrid a bara daga Juventus, ya kuma ci kwallo 20 a kakar da Real ta lashe kofin La Liga da na Zakarun Turai da ta kare.

Sai dai kuma dan kwallon bai buga wasa akai-akai a Real Madrid ba.

Morata shi ne na hudu da mai rike da kofin Premier Chelsea ta dauka a bana, bayan Tiemoue Bakayoko da Willy Caballero da kuma Antonio Rudiger.

Labarai masu alaka