Dan wasa daya zan saya saboda tsadar da suke yi — Mourinho

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mourinho ya taimaka wa kungiyarsa samun zuwa gasar Zakarun Turai bayan sun lashe Kofin Europa

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce wata kila ya kara sayen dan wasa guda daya domin kasuwar 'yan wasa tana da wuya.

Kocin ya ce kulob-kulob na tsawwala farashin 'yan wasa a kasuwar lokacin bazarar.

Mourinho ya ce: "Ba mu shirya wa biyan abin da kulob-kulob din suke so ba."

Tsohon kocin Chelsea, wanda ya sayi 'yan wasa biyu bayan ya bukaci sayen hudu: "Na saba ganin kulob-kulob na biyan makudan kudade wajen sayen 'yan wasa.

A halin yanzu kowa na biyan makudan kukade kan 'yan wasa masu kyau."

United ta kashe fam miliyan 75 kan dan wasan Everton, Romelu Lukaku, tare da kashe fam miliyan 31 kan dan wasan bayan Benfica, Victor Lindelof, tun karshen kakar bara.

Sayen dan asalin Belgium, Lukaku, ya sa jumullar kudin da kulob-kulob din gasar Firimiya suka kashe a kasuwar 'yan wasa ta wannan lokacin ya zarta fam miliyan 500.

Kamfanin lissafin kudi na Deloitte ya ce kungiyoyin gasar firimiya suna kan hanyar wuce tarihin da suka kafa na kashe fam dala biliyan 1.165 da suka kashe a lokacin bazarar da ta wuce.

Labarai masu alaka