West Ham na daf da daukar aron Hernandez

Hernandez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hernandez shi ne ya fi ci wa tawagar kwallon kafa ta Mexico kwallo

West Ham United ta kusa dauko aron dan kwallon Bayer Leverkusen, Javier Hernandez domin ya buga mata wasa.

West Ham tana da tabbacin son daukar tsohon dan kwallon Manchester United mai shekara 29, amma ba a fayyace kudin da za ta biya ba.

Hernandez ya ci kwallo 59 a wasa 156 da ya yi wa United wadda ya koma Old Trafford a 2010, daga nan ya koma Leverkusen a cikin watan Agustan 2015.

Dan kwallon da ake kira da sunan Chicarito ya yi wasa 76 a Jamus ya kuma ci kwallo 39.

Tuni kuma kungiyar ta shirya gwada lafiyar Marko Arnautovic, dan wasan da ta amince za ta dauka daga Stoke City.