AC Milan ta dauki Leonardo Bonucci

Juventus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bonucci ya yi shekara shida a Juventus wadda ta ci Serie A da aka kammala

Kungiyar AC Milan ta dauki Leonardo Bonucci kan kudi da ake cewa ya kai fan miliyan 40 daga Juventus.

Dan kwallon mai shekara 30, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku da Milan wadda ta kashe fan miliyan 160 wajen sayo 'yan wasa a bana.

Bonucci ya buga wa Juventus wasa kaka bakwai, inda ya yi fafatawa sau 319, ya kuma ci kofin Serie A shida a jere a kungiyar.

Juventus ce ta lashe kofin gasar Italiya da aka kammala kuma na shida a jere.

Ita kuwa Juventus ta kammala daukar Mattia de Sciglio mai shekara 24 daga AC Milan kan kudi fan miliyan 10.64.