An kara kasashen da za su buga kofin duniya zuwa 24

CAF
Bayanan hoto,

Za a buga gasar kofin Afirka a 2019 a Kamaru, kuma ita ce ke rike da shi

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka CAF, ta kara kasashen da za su fafata a gasar cin kofin nahiyar zuwa 24 da za a fara a wasannin da Kamaru za ta karbi bakunci a 2019.

Kwamitin zartarwa na hukumar CAF ne ya amince da wannan sauyin, bayan taron da ya gudanar a birnin Rabat na Morocco a ranar Alhamis.

CAF din ta maida gasar cin kofin Afirka ta kasashe 16 a shekarar 1996, sai dai kuma ba ta fayyace ko za ta gusar da wasannin da ake farawa a watan Janairu zuwa Fabrairu ta maida shi zuwa Yuni da Yuli ba.

Kamaru ce ke rike da kofin Afirka wanda ta lashe a shekarar nan a Gabon, kuma ita ce za ta karbi bakuncin wasannin da za a yi a 2019.