Ana taya Mbappe ta bayan gida - Monaco

Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mbappe ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Faransa wasa hudu

Monaco ta yi zargin cewar wasu kungiyoyin kwallon kafa na Turai suna tattaunawa da dan wasanta Kylian Mbappe ta bayan gida.

Kungiyar ta fitar da wani jawabi inda ta ce wasu manyan kungiyoyin Turai sun tuntubi dan kwallon mai shekara 18 ba tare da izininta ba.

Monaco za ta iya neman hakki a wajen hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, domin a hukunta wadanda take zargin idan aka same su da laifi.

Sashen wasanni na BBC ya fahimci cewar kungiyar Manchester City ce ake zargi, koda yake ta karyata hakan.

Tun a baya an alakanta cewar Monaco ba ta sallama tayin fan miliyan 87 da Arsenal ta yi wa Mbappeba.