Mutane uku sun mutu a boren Venezuela

Zanga-zangar Venezuela
Bayanan hoto,

'Yan adawa da gwamnatin shugaba Maduro ne suka shirya zanga-zangar da yajin aikin gama garin

Akalla mutane uku ne suka mutu a Venezuela yayin wata zanga-zanga da 'yan kasar suke yi a wani mataki na nuna fushinsu kan shirin gwamnati na sake tsarin kundin mulkin kasar sabo fil.

Miliyoyin 'yan kasar ne dai suka amsa kiran da bangaren masu hamayya ya yi na kowa da kowa ya zauna a gida a duka fadin kasar har tsawon awa 24, a wani yajin aiki irinsa na farko a tsawon shekara goma.

A wani jawabin da ya yi ta gidan talabijin, shugaba Nicholas Maduro ya ce babu gudu babu ja da baya, a inda ya ce tuni aka kakkama shugabannin da suka kitsa zanga-zangar.

'Yan adawar Venezuela ne dai ke iko da majalisar kasar, inda suke zargin ana amfani da kotun kolin kasar domin taimakawa gwamnatin shugaba Nicolás Maduro.

Fitar da sunayen sabbin alkalan wani sabon salon adawa ne da gwamanti da 'yan adawar ke yi. Kuma gwamnatin ta Venezuela ta ki amincewa da wannan matakin da suka dauka, amma matsin lamba na karuwa a kan shugaba Maduro gabanin zaben da za a yi nan da kimanin da mako guda mai zuwa.

A ranar Alhamis, ne 'yan adawar suka fara wani yajin aikin gama gari, suna fata wannan lamarin ka iya basu karin iko a cikin sabuwar majalisar.

Shugabannnin kasashe da dama sun soki matakan gwamnatin, kuma a ranar Laraba, shugabannin sun nuna damuwarsu game da tabarbarewar al'amura a Venezuelan.