Na yi farin cikin nasararmu kan Man City - Mourinho

Romelu Lukaku

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Romelu Lukaku ya ci kwllaye a wasanni biyun da ya buga wa Manchester United bayan ya koma taka mata leda

Nasarar da Manchester United ta yi kan Manchester City a birnin Houston a wasan sada zumunta "wani atisaye ne mai kyau", in ji kocin United, Jose Mourinho.

Romelu Lukaku da Marcus Rashford ne suka kwallayen a wasa na farko da kungiyoyin biyu suka yi a wajen Ingila.

Sabon dan wasa, Lukaku ya yanke mai tsaron gidan City, Ederson Moraes bayan Paul Pogba ya tura masa kwallo kuma ya sha kwallon minti 37 da fara wasa.

Bayan minti biyu sai Rashford ya tura kwallon da Jesse Lingard ya ba shi a raga.

"Na yi matukar farin ciki," in ji Mourinho.

"Na tabbata cewar Pep [Guardiola] yana jin dadi shi ma. Abu mafi muhimmanci shi ne a ba wa 'yan wasa horarwa mai kyau."

City ta kusa farke kwallo daya a lokacin da Sergio Romero ya ture kwallon da Fernandinho ya cilla sama. Kuma kociyan City, Guardiola ya ji dadin yanayin taka ledar dan wasan tsakiya mai shekara 17, Phil Foden, wanda ya fara taka wa manyan 'yan wasan kungiyarsa leda a wasan.

"Ba ni da kalaman da zan iya siffanta abun da na gani," in ji Guardiola. "Murza ledarsa ta kai wani mataki na mamaki. Yana kaunar kulob din. Magoyin bayan City ne. Wata bai wa ne garemu.

"Ta yi wu zai tsaya da mu a wannan kakar domin shi din dan wasa na musamman ne. Yana samar da damar shan kwallo, yana wuri mafi dacewa a ko da yaushe."

Wasan ne karon farko da kungiyoyin biyu suka hadu tun lokacin da aka kai hari a gidan rawar Manchester ranar 22 ga watan Mayu, kuma dukkansu sun saka riga mai dauke da kudan zuma.

Za a yi gwanjon rigunan da suka saka a wasan domin a yi amfani da kudin da za a samu wajen taimaka wa wadanda harin gidan rawar ya rutsa da su.