'Neymar, Sanchez da Matic za su sauya kulob'

Neymar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Neymar ya koma Barcelona a shekarar 2013 da kulob din Santos na Brazil

Dan wasan gaban Barcelona Neymar ya shaida wa takwarorinsa a kulob din cewa zai koma Paris St-Germain (PSG) kan fam miliyan 196, in ji jaridar Le Parisen ta Faransa.

Sai dai kocin Barcelona Ernesto Valverde ya ce maganar "jita-jita ce kawai" kuma suna so dan wasan ya ci gaba da kasance da su, kamar yadda jaridar Metro ta ruwaito.

Jaridar Mundo Deportivo a Spain ta ruwaito cewa Barcelona na son sayen dan wasan Juventus Paulo Dybala idan Neymar ya tafi.

Manchester City ta amince ta saye dan wasan Monaco Benjamin Mendy a kan fam miliyan 57, kamar yadda jaridar L'Equipe ta Faransa ta ruwaito.

PSG ta nuna sha'awar sayen dan wasan gaban Arsenal Alexis Sanchez a kan fam miliyan 70, in ji jaridar Daily Mirror ta Birtaniya.

Ita kuwa Manchester United ta taya dan wasan tsakiyan Chelsea Nemanja Matic ne a kan fam miliyan 35, sai dai Chelsea ta ce albarka; inda ta bukaci Man U ta biya fam miliyan 50, in ji Daily Mirror.

Real Madrid ta amince ta sayi dan wasan Monaco Kylian Mbappe a kan fam miliyan 120, in ji jaridar Sun.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mbappe mai shekara 18 ya fara takawa Monaco leda ne a shekarar 2015

Ita kuwa Barcelona gargadin dan wasan Liverpool Philippe Coutinho ta yi cewa idan ya ki amincewa ya koma can, to za su sayi dan wasan Borussia Dortmund Ousmane Dembele, a madadinsa, in ji Sun.

Arsenal tana zawarcin dan wasan tsakiyar Barcelona Rafinha a cewar kafar yada labarai ta Sky Sports.

Har ila yau, kulob din yana neman dan wasan bayan kungiyar Crystal Palace, Calum Chambers, kamar yadda jaridar Guardian ta ce.

Shi kuwa kocin Chelsea Antonio Conte yana zawarcin dan wasan gaban kungiyar Swansea Fernando Llorente, sai dai Swansea ta bukaci a biya fam miliyan 30 daga Chelsea, in ji jaridar Independent.

Hakazalika, Chelsea tana son sayen dan wasan tsakiyar Arsenal Alex Oxlade-Chamberlain a cewar Sky Sports.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Oxlade-Chamberlain ya koma Arsenal ne daga kungiyar Southampton a shekarar 2011

Kocin Newcastle Rafael Benitez ya ce yana neman sabon dan wasan gaba ne, kamar yadda jaridar Newcastle Chronicle ta bayyana.

Shi kuwa kocin Liverpool Jurgen Klopp cewa ya yi shi bai sallamar wa Barcelona Philippe Coutinho a kan fam miliyan 72 ba, kamar yadda jaridar Times ta bayyana.

A karshe jaridar Liverpool Echo ta ruwaito dan wasan Liverpool Joe Gomez yana cewa gara ya ci gaba da zama a Liverpool da ya je kungiyar Brighton a matsayin aro.