Man City na daf da daukar Danilo

Danilo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

City za ta dauki dan wasa Danilo kafin nan da ranan Litini

Ana sa ran Manchester City za ta kammala sayen dan wasan Real Madrid, Danilo kan kudi fan miliyan 26.5 nan da zuwa ranar Litinin.

Kocin Real, Zinedine Zidane ya ce dan kwallon mai shekara 26 mai buga wa tawagar Brazil tamaula ya bar inda kungiyar ke yin atisaye a Amurka ya ta fi City domin a duba lafiyarsa.

Sai dai an fahimci cewar har yanzun ba a gwada lafiyar dan wasan ba, kuma bai saka hannu kan yarjejeniya ba.

Ana sa ran Manchester City za ta kammala sayen Danilo kafin karawar da za ta yi da Real Madrid a ranar Laraba a gasar International Champions Cup a Amurka.