Ko Ronaldo, Mahrez da Sanchez za su sauya kulob?

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Madrid ta sayi Ronaldo daga Man U a kan fam miliyan 80 a shekarar 2009

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce ya yi amannar Cristiano Ronaldo "zai ci gaba da wasa" a Madrid bayan wasu rahotanni da suka ce dan wasan yana son barin Spain biyo bayan zarginsa da zambar haraji, in ji jaridar Independent.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya musanta labarin cewa dan wasansa Alexis Sanchez zai koma Paris St-Germain, kamar yadda jaridar Standard ta ruwaito.

Kocin Leicester City Craig Shakespeare shi ma cewa ya yi Riyad Mahrez zai ci gaba da wasa a kungiyar bayan wasu rahotannin da ke cewa Arsenal da Tottenham da kuma Roma suna zawarcinsa, in ji jaridar Leicester Mercury.

Mahrez zai ki amincewa da tayin fam miliyan 35 daga Roma a fatansa na ganin Arsenal ta saye shi a farashin da ya dara hakan, kamar yadda jaridar Sun ta ruwaito.

Liverpool da MAnchester City suna ci gaba da zawarcin dan wasan Monaco Kylian Mbappe, in ji Le 10 Sport.

Chelsea za ta gabatar da bukatar neman Alex Oxlade-Chamberlain ga Arsenal nan da kwana biyu, amma ita ma Manchester City tana zawarcin dan wasan tsakiyar mai shekara 23, in ji jaridar Sunday Express.

Har ila yau, kocin Chelsea Antonio Conte ya ce suna so su kara sayen 'yan wasa don kara karfafa kungiyar duk da cewa zuwa yanzu sun kashe kimanin fam miliyan 130 wajen sayen sabbin 'yan wasa, in ji Sunday Telegraph.

Paris St-Germain suna ci gaba zawarcin dan wasan gaban Barcelona Neymar inda suka tayi shi a kan fam miliyan 196, in ji Sunday Express.

Jaridar Sunday Mirror ta ce Barcelona ta shirye tsaf don sayen dan wsan Liverpool Philippe Coutinho a kan fam miliyan 80.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Coutinho mai shekara 25 ya koma Liverpool ne a shekarar 2013 daga Inter Milan

Sai dai kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce Coutinho "yana jin dadin zama" a kungiyar bayan ya gana da dan wasan game da maganar komawarsa Barcelona, in ji kafar yada labarai ta ESPN FC.

Sabon dan wasan da Manchester United ta saya, Victor Lindelof, ya ce "dangantakata da kocin kungiyar Jose Mourinho tana kara kyautatuwa ne a kullum " , in ji Manchester Evening News.

Har ila yau, jaridar Guardian ta ce Manchester United tana ci gaba da zawarcin dan wasan tsakiyan Chelsea Nemanja Matic bayan sun rasa dan wsan Tottenham Eric Dier.

United ta dakatar da maganar sayo dan wasan tsakiyar Paris St-Germain (PSG) Marco Verratti saboda yadda PSG din ta bukaci su yi musayansa da Anthony Martial, in ji Sunday Mirror.