De Gea zai ci gaba da zama a Old Trafford

De Gea

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Real Madrid ta amince ta dauki De Gea kan kudi fan miliyan 29 a 2015 a ranar da za a rufe kasuwar sayen 'yan wasan tamaula ta Turai

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya bayar da tabbacin cewar David de Gea zai ciga da wasa a Old Trafford a bana.

Ana alakanta De Gea mai shekara 26, da cewar zai koma Real Madrid da murza-leda shekara biyu bayan da kungiyar ta yi lattin cike takardun ka'ida da ya kamata ya koma Spain da wasa.

Mourinho ya ce a bara sun yi kokarin sayarwa da Madrid mai tsaron ragar, amma yanzu sun sauya shawara zai ci gaba da zamansa a United.

Haka kuma a makon jiya Cristiano Ronaldo ya karyata rade-radin da ake cewar zai sake komawa Manchester United da buga tamaula.