Za mu rike Neymar duk runtsi — Valverve

Barcelona

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Neymar ya tsawaita ci gaba da zama a Barcelona har zuwa karshen kakar 2021

Kociyan Barcelona, Ernesto Valverde ya ce za su hana Neymar barin kungiyar a bana, bayan da dan wasan ya ci kwallo biyu a karawa da Juventus a wasan sada zumunta.

An ce Paris St-Germain za ta biya Yuro miliyan 222 kudin ka'ida da Barca ta ajiye idan wani kulob din na son daukar dan kwallo kafin yarjejeniyarsa ta kare a Camp Nou.

Sai dai kuma shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu ya shaidawa sashen wasanni na BBC cewar ba za su sayar da Neymar mai shekara 25 ba.

Neymar bai tattauna da 'yan jarida bayan da Barcelona ta ci Juventus 2-1 ba a New Jersey, amma Valverve ya yi bayanai kan batun Neymar.

Neymar ya koma Barcelona da taka-leda a 2013 daga Santos ya kuma sabunta yarjejeniyarsa ci gaba da zama a Camp Nou zuwa 2021.