Dan Aminu ya buge Shagon Abata mai

Damben gargajiya
Bayanan hoto,

Dan Aminu da Shagon Abata mai a turmin farko suka kammala damben

Dambe 12 aka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja. Nigeria a safiyar Lahadi.

Cikin wasan har da wanda ya zo da takaddama tsakanin Dan Aminu Langa-Langa daga Arewa da Shagon Abata mai daga Kudu.

A cikin turmin farko Dan Aminu ya yi nasara a kan Shagon Abata mai, amma magoya baya suka ce ture aka yi a fafatawar, daga baya aka sasanta aka bayar da kisan.

Shagon Abata mai ya sake dambe a karo na biyu amma da Nuran Dogon Sani daga Arewa, inda a turmi na biyu sai da Audu Dan Crispo ya kawowa Nuran dauki a damben sai dai babu kisa suka kare.

Tun farko Shagon Shagon Abata mai daga Kudu ya buge Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da wasan da Shagon Bahagon Sico daga Kudu ya yi nasara a kan Shagon Buzu daga Arewa a turmin farko.