Jaridar Daily Mirror ta wallafa cewar Barcelona za ta dauki Coutinho

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dan wasan Liverpool Coutinho wanda ke kan ganiyarsa

Daily Mirror wadda ta wallafa cewar a shirye Barcelona take ta sayi Philippe Coutinho daga Liverpool kan kudi fan miliyan 80.

Ita kuwa Daily Mail cewa ta yi Barcelona ta hakikance cewar idan ta dauko Coutinho daga Liverpool zai taimaka Neymar wanda PSG ke zawarci ya ci gaba da zama a Camp Nou.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya karyata rade-radin da ake cewar Alexis Sanchez na daf da komawa Paris St-Germain kan kudi fan miliyan 70.

Independent kuwa cewa ta yi kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya hakikance cewar Cristiano Ronaldo zai ci gaba da taka-leda a kungiyar duk da rahotonnin da ake cewar zai bar Spaniya da wasa sakamakon zargin kin biyan haraji da ake yi masa.

ita kuwa Daily Express cewa ta yi Chelsea za ta yi zawarcin dan wasan Arsenal, Alex Oxlade-Chamberlain, wanda Manchester City ke son saye.