Zan ci gaba da zama daram a Arsenal - Koscielny

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mai tsaron bayan ya koma Arsenal a 2010

Mai tsaron bayan Arsenal, Laurent Koscielny ya ce ba shi da niyar barin kungiyar, bayan da ake rade-radin cewar Marseille na son daukar dan kwallon.

Koscielny mai shekara 31, ya koma Arsenal daga Lorient a 2010, ya kuma saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da wasa a Emirates zuwa watan Janairun 2020.

Mai tsaron bayan wanda ya buga wa Arsenal wasa sama da 200, ya ce "Wenger ya daraja shi domin shi ne ya kai shi Arsenal ya kuma taimaka masa ya kai ganiya a tamaula".

Arsenal wadda ke yin wasannin atisaye a Australia da China domin tunkarar kakar wasan da za a fara ta dauki Alexandre Lacazette daga Lyon da kuma Sead Kolasinac daga Schalke a bana.