Man City ta dauki dan wasa na biyar a bana

Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mendy shi ne na biyar da ya koma City a bana

Manchester City ta kammala sayen mai tsaron baya na Monaco, Benjamin Mendy kan kudi fan miliyan 52 kuma na biyar da ta dauka a bana.

Dan wasan mai shekara 23, wanda ya koma Monaco daga Marseille a bara ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar.

Mendy shi ne dan kwallo na biyar da City ta dauka a bana, wanda ta kashe fan miliyan 200 wajen sayo 'yan wasan.

City ta sayi Kyle Walker kan fan miliyan 45 da mai wasan tsakiya Bernardo Silva kan fan miliyan 43 da mai tsaron raga Ederson Moraes kan fan miliyan 35 da kuma Danilo kan fan miliyan 26.5.

Haka kuma kungiyar ta Ettihad ta sayar da Aleksandar Kolarov ga Roma kan kudi fan miliyan 4.5.