Inter Milan za ta iya sayar da Ivan Perisic ga Man United

Ivan Perisic

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ivan Perisic ya ci kwallo 18 a gasar Serie A cikin kaka biyu a Italiya

Kociyan Inter Milan Luciano Spalletti ya ce kulob din zai yarda ya sayar da dan wasan gefe Ivan Perisic, idan aka yi masa kakkyawan tayi.

An na rade-radin cewar dan wasan gefen dan asalin Crotia zai koma Manchester United kan kudi fan miliyan 48.

Spalletti ya ce Inter tana son Perisic, mai shekara 28, ya tsaya, amman za su sayar da tsohon dan wasan na Wolfsburg domin samun kudin da za su sayi sabbin 'yan wasa.

"Yana da muhimmanci a cikin 'yan wasanmu kuma muna sa ran zai fara mana wasa a sabuwar kaka," in ji tsohon kociyan na Roma.

Spalletti, wanda aka nada a matsayin kociyan Inter a watan Yuni, ya kara da cewar: "Da gaske akwai rade-radi, amman a halin yanzu dai muna son Perisic ya tsaya.

"Baya ga haka, idan wani ya zo ya taya shi da irin kudin da ba za mu iya raina wa ba, za mu iya sayar da shi.

"Amman kuma za mu nemi mu samu wanda ka iya maye gurbin Perisic."

Wakilan United sun ziyarci Milan domin su tattauna kan wata yarjejeniya ta dan wasan.

Perisic ya ci kwallo18 a wasanni 70 da ya buga a gasar Serie A tun lokacin da bar Wolfsburg ta Jamus zuwa Italiya kan kudin da aka ce ya kai fan miliyan 14.5 a watan Augustan 2015.