Sanchez zai koma Arsenal ranar Lahadi

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sanchez ya yi hutu bayan da ya buga wa Chile Confederation Cup

Bayan da ake ta samun rahotannin da ke cewar Alexis Sanchez zai bar Arsenal a bana, Arsene Wenger ya sanar da cewar dan kwallon Chilen zai koma atisaye a ranar Lahadi.

Sanchez bai buga wa Arsenal wasannin atisayen tunkarar kakar bana da ta yi a Australia da China ba, sakamakon hutun da ya yi, bayan da ya buga wa Chile Confederations Cup.

A karshen kakar badi yarjejeniyar Sanchez za ta kare da Arsenal kuma bai saka hannu kan sabon kwantiragi ba.

Sanchez ya bukaci Arsenal ta biya shi Yuro 300,000 a duk mako, kafin ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniya, abin da kungiyar ta ce ba za ta iya biya ba.

Hakan ne ya sa ake cewa dan kwallon zai iya komawa Paris Saint Germain ko Manchester City ko Juventus ko kuma Bayern Munich da taka-leda.

Shi ma Shkodran Mustafi zai koma atisaye a ranar Lahadi, bayan da ya gama hutun murnar lashe Confederation Cup da Jamus ta yi.