Ina Lemar da Bale da Keita da Coutinho da Barkley za su koma?

Thomas Lemar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A yanzu dai Thomas Lemar yana taka leda ne wa kungiyar kwallon kafa ta Monaco

Latsa nan domin sanin cinikin 'yan wasan da aka kammala a turance.

Labaran cinikin 'yan wasa

Arsenal na dab da sayen Thomas Lemar daga Monaco kan Fam miliyan 45m . (Sun)

Kociyan Real Madrid, Zinedine Zidane, ya ce ba zai iya tabbatar da cewar dan wasan gaban nan, Gareth Bale, mai shekara 28- wanda Manchester United take so- zai tsaya Bernabeu ba a lokacin bazarar nan. (Mirror)

Kociyan Chelsea, Antonio Conte, na shirin sayan 'yan wasan tsakiyar Ingila biyu - dan Everton, Ross Barkley da kuma dan Arsenal, Alex Oxlade-Chamberlain. (Sun)

Jagoran Tottenham, Mauricio Pochettino, yana son ya sayi Barkley a lokacin bazaran nan domin ya mayar da shi dan wasan tsakiya. (Times - subscription required)

Roma ta shirya sake tayin dan wasan Leicester City kuma dan asalin Aljeriya Riyad Mahrez, mai shekara 26 kan Fam miliyan 32.(Mirror)

Chelsea ta yi tayin dan wasan tsakiyan Bayern Munich, Renato Sanches kan bashi. (Telegraph)

Liverpool ta shirya domin ta yi tayin karshe wa dan wasan tsakiyan Guinea Naby Keita kan sama da Fam miliyan 70.(Mirror)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Philippe Coutinho yana taka leda ne a Liverpool a halin yanzu

Har ila yau, Reds na kan bakansu cewar dan wasan gaban Brazil, Philippe Coutinho, mai shekara 25, ba na sayarwa ba ne a dadai lokacin da Barcelona ke sha'awar sayansa.(ESPN)

Kociyan Inter Milan, Luciano Spalletti ya ce yana son dan asalin Croatia mai shekara 28, Ivan Perisic - wanda Manchester United ke hako- ya tsaya a kulob din, amma shi ba zai iya tabbatar da abin da zai faru ba. (ESPN)

Juventus ta mayar da hankalinta kan dan wasan Paris St-Germain, Blaise Matuidi, mai shekara 30, yayin da suke neman sayan dan wasan tsakiya mai tsaron baya, lamarain da ya sake saukaka wa Manchester United da Chelsea hanyar sayen dan wasan tsakiya, dan asalin kasar Serbi, Nemanja Matic, mai shekara 28.(Independent)

Shugaban AC Milan, Marco Fassone ya bayyana cewar kungiyar ta tuntubi wakilin dan wasan kungiyar Chelsea dan asalin Spaniya, Diego Costa, mai shekara 28. (Sky Sports)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kylian Mbappe mai shekara 18 na taka leda ne a Monaco

Ana tsammanin dan wasan gaba, Karim Benzema, mai shekara 29, zai sake kulla yarjejeniya da Real Madrid domin kaka mai zuwa ko kulob dinsa ya sayi dan wasan Monaco mai shekara 18, Kylian Mbappe, ko bai saya ba.(Marca)

Dan wasan gaban Argentina,Paulo Dybala, mai shekara 23 - wanda Manchester United da Barcelona ke hako- ba shi da niyyar barin Juventus a lokacin bazarannan.(Talksport)

Agen din Lucas Perez ya kai ziyara Landan domin tattaunawa kan komawar dan wasan gaba dan asalin Spaniyan mai shekara 28 zuwa Deportivo La Coruna.(AS)

Tsohon dan wasan gefe na Arsenal da Liverpool, Jermaine Pennant, mai shekara 34, ya shirya domin rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Billericay Town duk da cewar kungiyar kwallon kafa ta gasar Firimiyar Scotland, Hibernian na son sayan sa. (Sun)