Ashley Fletcher: Middlesbrough ta sayi dan wasan West Ham

Ashley Fletcher Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ashley Fletcher ya si nasara a bahsin da ya tafi Barnsley a kakar 2015-16

Middlesbrough ta sayi dan wasan gaban West Ham United, Ashley Fletcher, a yarjejeniyar shekara hudu kan Fam miliyan 6.5.

Fletcher, mai shekara 21, ya bar sansanin atisayen Hammers a Jamus ne ranar Alhamis domin som tattaunawa da kungiyar da ke gasar Championship.

Kawo yanzu Boro ta kashe kimanin Fam miliyan 30 kan 'yan wasan gaba a lokacin bazaran nan bayan ta riga ya ta sayi Britt Assombalonga da Martin Braithwaite.

Fletcher, wanda ya koma West Ham daga Manchester United a shekarar 2016, ya ci kwallo daya a wasanni 20 da ya buga wa Hammers.

A lokacin da ya je Barnsley kan bashi a kakar 2015-16, Fletcher ya ci kwallaye takwas a wasanni 27 da ya yi wa Tykes yayin da suka samu hayewa zuwa gasar Championship.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba