Wanne kulob ne zai lashe gasar Premier ta bana?

Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea ce ta lashe kofin Premier na 2016/17 kuma na shida jumulla

A ranar 12 ga watan Agusta ne za a fara gasar Premier ta 2017/18, kuma tuni kulob-kulob suka fara daura damara domin tunkarar gasar.

Kawo yanzu an kashe kusan fam biliyan daya wajen sayen sabbin 'yan wasa.

Kungiyoyi 20 ne za su fafata a wasannin da za a fara, inda ake sa ran uku za su bar gasar, kuma tuni suka tashi tsaye wajen shirye-shiryen yadda za su taka rawar gani.

Shin wacce kungiya ce za ta dauki kofin kakar bana ta 2017/18.

Manchester City ta kashe fiye da fam miliyan 200, takwararta United ta kashe sama da fam miliyan 100, Everton kuwa fam miliyan 90 ta kashe, yayin da Swansea City ta yi wa Gylfi Sigurdsson kudi fam miliyan 50.

Tuni aka kashe fiye da fan miliyan 580 wajen saye da sayar da 'yan wasa a gasar Premier tun lokacin da aka kammala kakar da ta kare.

Kamfanin Deloitte ya ce za a sake kafa tarihin kashe kudade da dama kafin a rufe kasuwar ciniki a tsakar daren ranar 31 ga watan Agusta.

Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Yadda ake saye da sayar da 'yan wasan gasar Premier

'Yan wasa nawa Chelsea ta saya a bana?

Chelsea ce ta lashe kofin Premier da aka kare, kuma kakar farko da koci Antonio Conte ya ja ragamar kungiyar da ke buga wasanninta a Stamford Bridge.

Hakan ne ya sa ta dauko sabbin 'yan wasa a bana:

 1. Willy Caballero (Manchester City)
 2. Rudiger (Roma, Yuro miliyan 35),
 3. Bakoyoko (Monaco, Yuro miliyan 40),
 4. Morata (Real Madrid, Fam miliyan 80)

Cikin wasannin atisayen da ta yi ta doke Arsenal 3-0, ta yi rashin nasara da ci 3-2 a hannun Bayern Munich.

Har ila yau, Chelsea ta ce ba za ta yi amfani da Diego Costa ba a kakar da za a fara duk da kwallayen da ya ci wa kungiyar da suka ba ta nasarar cin kofin Premier.

Tottenham ce ta yi ta biyu a gasar Premier bara, sai dai kuma ana ganin kungiyar na son yi wa kanta sakiyar da babu ruwa, ganin har yanzu ba ta sayi dan kwallo ba, amma kuma ta sayar da wasu.

 1. Bentaleb (Schalke, Yuro miliyan 19),
 2. Fazio (Roma, Yuro miliyan 3.2),
 3. N'Jie (Marseille, Yuro miliyan 7),
 4. Kyle Walker (Manchester City, Yuro miliyan 56.7)

Tottenham za ta buga gasar Premier da ta Zakarun Turai da FA Cup da League a shekarar nan.

Manchester City ce ta yi ta uku a gasar Premier da aka kammala, kuma ta buga wasan atisayen tunkarar kakar bana da Manchester United, inda ta yi rashin nasara da ci 2-0.

Sai dai ta doke Real Madrid da ci 4-1 a gasar International Champions Cup a Amurka.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption AC Milan na son daukar Costa, shi kuwa so yake ya koma Athletico Madrid

Shin wadanne 'yan wasa Manchester City ta dauka a bana?

 1. Bernardo Silva (Monaco, Yuro miliyan 50),
 2. Ederson (Benfica, Yuro miliyan 40),
 3. Kyle Walker (Tottenham, Yuro miliyan 56.7),
 4. Danilo (Real Madrid, Yuro miliyan 30)
 5. Benjamin Mendy (monaco, fan miliyan 52)

Pep Guardiola na fatan City za ta taka rawar da ta dace a wasannin da za a fara, ganin cewa kakar farko bai tabuka abin a zo a gani ba duk da irin nasarorin da ya yi a Barcelona da Bayern Munich.

Rabon da Liverpool ta dauki kofin Premier tun 1989/90 kuma har yanzu tana fatan ta ci Premier bayan da ta yi ta uku a kakar da ta kare, hakan ne ya sa kungiyar za ta buga wasannin cike gurbin shiga gasar Zakarun Turai da FA Cup da League Cup a kakar da za a fara.

Tuni kungiyar ta dauki 'yan wasa da suka hada da

 1. Salah (Roma, Yuro miliyan 42),
 2. Solanke (Chelsea),
 3. Robertson (Hull City)

A kakar da ta kare Arsenal ta kammala gasar a mataki na biyar a teburi, wanda rabon da ta yi hakan tun shekara 20, hakan ya sa kungiyar za ta buga gasar Zakarun Turai ta Europa bayan da ta je gasar Champions League 20 a jere.

Da kyar magoya bayan Arsenal suka amince kungiyar ta tsawaita zaman Arsene Wenger a kungiyar, wanda yanzu zai kara kaka biyu a Gunners.

Rabon da Arsenal ta ci kofin Premier tun kakar 2002/03.

Hakan ne ya sa Arsenal ta sayo sabbin yan wasa tana kuma ci gaba da zawarcin wasu.

 1. Kolasinac (Schalke),
 2. Lacazette (Lyon, Yuro miliyan 53)

Manchester United ta shida ta yi a Premier 2016/17, sai dai kungiyar ta ci Europa League wanda ya ba ta damar shiga gasar kofin Zakarun Turai da za a yi ta bana, hakazalika za ta yi gumurzi a FA Cup da League Cup.

A karshen kakar da ta kare yarjejeniyar Zlatan Ibrahimovic ta kare da Manchester United, kuma kungiyar ba ta kulla sabuwar yarjejeniya da dan wasan ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ibrahimovic ya taka rawar a Manchester United a kakar da ta kare

Tuni dai United ta sayi 'yan wasa da suka hada da

 1. Lindelof (Benfica, Yuro miliyan 35),
 2. Lukaku (Everton, Yuro miliyan 85)

Sauran kungiyoyin da ake ganin za su taka rawa a Premier da za a fara sun hada da Everton da Southampton da West Brom da West Ham wadanda su ma suka daura damarar shiga gasar bana.

Leicester ma ta yi sayayya, ita ma Swansea wadda da kyar ta sha a bara na fatan yin abin kirki a bana.

Newcastle United wadda ta dawo gasar Premier tana daga cikin sabbin da ake sa ran yin abin azo a gani a shekarar nan.

Kungiyar Chelsea ce ta lashe gasar da aka kammala ta 2016/17, wadda bayan da aka buga wasa 38 a gasar, ta ci 30, ta yi canjaras a karawa uku, aka doke ta sau biyar.

Jerin kungiyoyin da suke 10 farko bayan da Chelsea ta lashe kofin

 • 2 Tottenham Hotspur 86
 • 3 Manchester City 78
 • 4 Liverpool 76
 • 5 Arsenal 75
 • 6 Manchester United 69
 • 7 Everton 61
 • 8 Southampton 46
 • 9 Bournemouth 46
 • 10 West Bromwich Albion 46

Kungiyoyin da suka fi yawan daukar Premier a tarihi

 • 20 Manchester United
 • 18 Liverpool
 • 13 Arsenal FC
 • 9 Everton FC
 • 7 Aston Villa
 • 6 Chelsea FC
 • 6 Sunderland
 • 4 Manchester City
 • 4 Sheffield Wednesday FC
 • 4 Newcastle United FC
 • 3 Blackburn Rovers FC
 • 3 Leeds United FC
 • 3 Wolverhampton Wanderers FC
 • 3 Huddersfield Town
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Magoya bayan kungiyar Brighton & Hove Albion

Sabbin kungiyoyin da za su buga gasar 2017/18

Kungiyar da ta fara samun tikitin shiga gasar Premier ta bana ita ce Brighton & Hove Albion, bayan da ta doke Wigan Athletic da ci 2-1.

Wannan ne karon farko da Brighton za ta buga babbar gasa a tarihin kwallon kafar Ingila tun 1983, kuma wannan ce gasar Premier ta farko da za ta fafata.

Kulob na biyu da ya samu tikitin shiga Premier na bana shi ne Newcastle United, bayan da ya doke Preston North End 4-1 a gida a ranar 24 ga watan Afirilu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Newcastle United ce ta lashe gasar Championship

Ta uku da ta samu gurbin shiga Premier shekarar nan ita ce Huddersfield Town, wadda ta ci Reading 4-3 a bugun fenariti, bayan da suka tashi wasa babu ci a fafatawar cike gurbi.

Wannan ne karon farko da kungiyar za ta buga babbar gasar Ingila tun bayan shekara 45, kuma karon farko da za a yi gumurzu da ita a wasannin Premier.