Real Madrid za ta yi wasa shida a Agusta

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ce mai rike da kofin Zakarun Turai da na La Liga a kakar da ta kare

Da zarar Real Madrid ta kammala wasannin atisayen tunkarar kakar bana da take yi a Amurka, za ta mayar da hankali wajen lashe kofi biyu da suke gabanta a Agusta.

Real za ta buga wasan sada zumunta da fitattun 'yan wasan da suke buga gasar Amurka a ranar Alhamis 3 ga watan Agusta, kuma shi ne na karshe da za ta yi sannan ta koma Spaniya.

Daga nan ne Real Madrid za ta kara da Manchester United a UEFA Super Cup a Macedonia a ranar Talata 8 ga watan Agusta.

Kwanaki biyar tsakani Madrid za ta ziyarci Barcelona a wasan farko a gasar Spanish Super Cup, wanda ake karawa tsakanin Zakaran La Liga, Real da na Copa del Rey, Barca.

Barcelona za ta halarci Santiago Bernabeu a gumurzu na biyu a ranar 16 ga watan Agusta a gasar ta Spanish Super Cup.

Daga nan Real za ta fafata a wasan farko a gasar La Liga a ranar 20 ga watan Agusta da Deportivo La Coruna, sannan ta buga karawar mako na biyu a gida da Valencia a ranar 27 ga watan.

Labarai masu alaka