Damben Nuran dogon Sani da na Abata Mai
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Turmi biyu suka dambata babu kisa aka raba

Damben da aka yi tsakanin Nuran Dogon Sani daga Arewa da Shagon Abata Mai daga Kudu, turmi biyun da suka kara babu kisa a safiyar Lahadi a unguwar Dei-Dei da ke Abuja, Najeriya.

Mohammed Abdu ne ya hada rahotan

Wasanni 12 aka dambata a gidan wasa na Ali Zuma da ke Abuja a safiyar Lahadi, inda aka yi kisa a karawa uku sauran aka tashi canjaras.

Ga wasannin da aka yi kisa:

 1. Dan Shagon Abata Mai daga Kudu ya buge Shagon Ali Kanin Bello daga Arewa
 2. Shagon Ali Kanin Bello daga Arewa ya doke Gulafa Shagon Wale daga Kudu
 3. Bahagon Sama'ila daga Kudu ya yi nasara a kan Bahagon Katsinawa daga Arewa.

Wasannin da babu kisa:

 1. Shagon Bahagon Balan Gada daga Arewa da Shagon Bahagon Fandam daga Kudu
 2. Bahagon Katsinawa daga Arewa da Shagon Dogon Jamilu daga Kudu
 3. Dan Yellow Gusau daga Arewa da Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu
 4. Dan Shagon Abata Mai daga Kudu da Shagon Shagon Buzu daga Arewa
 5. Shagon Inda daga Arewa da Shagon Shagon Abata Mai daga Kudu
 6. Bahagon Sama'ila daga Kudu da Shagon Shagon Bahagon Musa daga Arewa
 7. Shagon Dan Jamilu daga Kudu da Shagon Cika aiki daga Arewa
 8. Shagon Shagon Lawwali daga Arewa da Dan Shagon Abata Mai daga Kudu

Labarai masu alaka