Arsenal ta sake lashe Emirates Cup

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal ta lashe Emirates Cup duk da rashin nasara da ta yi a hannun Sevilla

Kungiyar Arsenal ta sake lashe Emirates Cup na bana, duk da rashin nasara da ta yi a hannun Sevilla da ci 2-1 a wasan karshe da suka fafata a yammacin Lahadi.

Sevilla ta ci kwallo ta hannun Joaquin Correa da kuma Steven N'Zonzi, ita kuwa Arsenal ta zare daya ta hannun Alexandre Lacazette wanda ta dauko a bana daga Lyon.

Arsenal ta ci kofin na bana duk da doke ta da aka yi, bayan da dokar wasan ta ce yawan cin kwallo shi ne yawan maki.

Sevilla ta fara cin RB Leipzig daya mai ban haushi da kuma doke Arsenal 2-1, ita kuwa Gunners ta cin Benfica 5-2, sannan ta yi rashin nasara a hannun Sevilla.

Saboda haka Arsenal ce ta daya a kan teburi da kwallaye shida, sai Sevilla ta biyu biye da ita.

Arsenal za ta kara da Chelsea a Community Shield a Wembley ranar 6 ga watan Agusta, daga nan ta fara buga gasar Premier da Leicester City kwana biyar tsakani.

Labarai masu alaka