Coutinho zai zauna a Liverpool

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona na son ta maye gurbin Neymar da Coutinho

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce ba za su sayar da Philippe Coutinho ga Barcelona duk da zawarcin da take yi wa dan wasan ba.

Klopp ya ce Liverpool ba kungiyar sayar da 'yan wasa ba ce, bayan da ake rade-radin cewar ta ki sallama tayin fam miliyan 72 da aka yi wa dan wasan tawagar Brazil.

Coutinho shi ne kyaftin din Liverpool a karawar da ta ci Hertha Berlin 3-0 a wasan sada zumunta a ranar Asabar.

Ana sa ran dan kwallon zai buga fafatawar da Liverpool za ta yi da Bayern Munich a gasar Audi Cup a ranar Talata.

Labarai masu alaka