Liverpool ta doke Bayern Munich 3-0

Daniel Sturridge Hakkin mallakar hoto Rex Features

Liverpool ta doke Bayern Munich da ci 3-0 a wasan kusa da na karshe na gasar Audi Cup.

Sai dan wasan gabanta Daniel Sturridge, wanda ya zira kwallo ta uku, ya samu rauni.

An maye gurbinsa a minti na 87, inda koci Jurgen Klopp ya ce yana fatan raunin "ba mai muni ba ne".

Sadio Mane da Mohamed Salah ne suka zura sauran kwallo biyun, wanda hakan ya bai wa Liverpool damar karawa da Atletico Madrid a wasan karshe ranar Laraba.

Mane ne ya fara zira kwallon farko a minti na shida bayan wata dabara da Roberto Firmino ya yi.

Sannan kuma dan wasan na Senegal ya taimaka wa Salah ya zira kwallo ta biyu.

Labarai masu alaka