Dole a rage shan miyagun kwayoyi a wasanni - Bolt

Usain Bolt
Image caption Usain Bolt na da magoya baya da dama a duniya

Zakaran tseren duniya Usain Bolt ya ce dole 'yan wasa su rage shan miyagun kwayoyi a daidai lokacin da yake shirin tunkarar gasarsa ta karshe.

Bolt, wanda ya lashe lambar zinare sau takwas a gasar Olympic, kuma wanda ake wa kallon gagara-badau a fagen wasanni, zai yi ritaya bayan gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da za a yi a wannan watan.

Dan wasan kasar Jamaica, mai shekara 30, zai yi gudu a tseren mita 100 da kuma 4x100m a gasar, wacce za a fara a birnin Landan ranar Juma'a.

Ya ce: "Ina fatan 'yan wasa za su yi la'akari da abin da yake faruwa da kuma abin da ya kamata su yi su ciyar da wasan gaba".

Bolt ya lashe tseren 100m, 200m da 4x100m a gasar Olympic uku da ta gabata a jere - Beijing 2008, London 2012 da kuma Rio 2016.

Sai dai ya rasa lambarsa ta zinare guda daya bayan da aka samu daya daga cikin 'yna tawagar Jamaica ta 4x100m a Beijing Nesta Carter, da laifin amfani da kwayoyin da aka haramta.

Labarai masu alaka