Jiragen Ethiopia sun fara tashi daga Kaduna

Kaduna Hakkin mallakar hoto Twitter/ Ethiopian Airlines
Image caption kaduna ya zama birnin sauka da tashi na biyar da kamafin jiragen saman na Ethiopian Airlines ke amfani da shi

Kamfanin jirgin sama na kasar Habasha, Ethiopian Airline, ya fara tashi daga birnin Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya domin tafiyar kasa-da-kasa.

A ranar Talata ne jirgin farko na kamfanin jiragen ya tashi daga Kaduna, lamarin da masu hanu da tsaki a harkar jiragen sama ke cewa zai taimaka wa mazauna birnin da wasu garuruwa makwabta damar fara tafiyat kasa-da-kasa ba tare da sun tafi Abuja ko Legas ba kafin su yi tafiya.

Filin sauka da tashin na jiragen sama na Kaduna shi ne fili na biyar da kamfanin na Ethionpian Airlines ya bude na sauka da tashi daga Najeriya.

Ko a kwanakin baya ma da gwamnatin tarayyar Najeriya ta rufe filin tashi da sauka na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja domin gyara, Ethiopia Airlines ce jirgin kasa da kasa da ta fara komawa Kaduna tashi da sauka kamar yadda gwamnatin kasar ta bukata.

Labarai masu alaka