Neymar zai fi kowa daukar albashi

Neymar Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An dade ana ce-ce-ku-ce a kan makomar Neymar

Dan wasan gaba na Brazil Neymar zai ringa daukar fan 775,477 a kowanne mako idan ya koma Paris St-Germain daga Barcelona.

Cinikin dan kwallo da PSG za ta yi, shi ne zai kasance mafi tsada a duniya.

Jumullar albashin da zai rinka samu zai kai fan miliyan 40 a kowacce shekara kafin biyan haraji.

Barcelona ta shaida wa PSG cewa dole ne su biya fan miliyan 198 na sayen dan wasan lakadan.

Wannan na nufin jumullar abin da PSG za su kashe a shekara biyar din farko da Neymar zai yi a can zai kai fan miliyan 400.

Nan da mako daya ake sa ran kammala wannan ciniki.

A ranar Laraba ne dan wasan ya shaida wa Barcelona cewa yana so ya bar kungiyar.

Daga nan ne kuma koci Ernesto Valverde ya bashi izinin ficewa daga filin atisaye domin ya mayar da hankali kan batun makomarsa.

Labarai masu alaka