Tsohon zakaran boksin Klitschko ya yi murabus

Wladimir Klitschko and Anthony Joshua Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Klitschko ya sha kaye a damben boksin a hannun Anthony Joshua a fafatawar da suka yi a filin wasa na Wembley a watan Afrilu

Tsohon zakaran damben boksin ajin masu nauyi, Wladimir Klitschko, ya yi murabus daga damben boksin - yana mai cewa ba zai sake fada da dan Birtaniya, kuma dan asalin Najeriya, Anthony Joshua.

Dan asalin kasar Ukrain din, mai shekara 41, ya sha kaye a turmi na 11 daga hannun zakaran damben na yanzu a filin wasa na Wembley a watan Afrilu.

Joshua, mai shekara 27, ya yi fatan cewar Klitschko zai yarda ya sake karawa da shi a wani damben da za su yi a birnin Las Vegas ranar 11 ga watan Nuwamba.

Klitschko ya ce: "Na cimma dukkan abubuwan da na so in samu, kuma yanzu ina son in fara aikina na biyu bayan wasan motsa jiki."

Klitschko, wanda ya ci kambun damben boksin ajin masu nauyi sau biyu, kuma ya rike hadadden kambun daga shekarar 2006 zuwa 2015 kafin ya sha kaye a ahnnun wani dan Birtaniyan daban, Tyson Fury, ya kawo karshen dambensa ne yana da nasara 64 da kuma shan kaye biyar.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba