Sanchez zai yi zamansa a Arsenal — Wenger

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester City da PSG ne ke son daukar Sanchez daga Arsenal

Alexis Sanchez zai ci gaba da taka-leda a Arsenal a kakar bana, kuma zai martaba hakan in ji koci Arsene Wenger.

Rahotanni na cewa Manchester City da Paris St-Germain na zawarcin Sanchez mai shekara 28, bayan da yarjejeniyarsa da Arsenal za ta kare a kakar shekarar da za a fara.

Dan wasan ya koma atisaye a Gunners a ranar Talata, bayan da aka tsawaita masa hutun buga wa Chile gasar Confederation Cup da ya yi, sakamakon rashin lafiya da ya yi.

Wenger ya ce ''Ba zan sake magana ko hira a cikin jama'a kan makomar Sanchez ba, domin yanzu ba wani sabon labari bane, kamar mutun ya burma kansa ne''.

Wenger ya kuma tabbatar da cewar zai amince Lucas Perez ya bar Gunners wanda tsohon kulob dinsa Deportivo La Coruna ke zawarci.