Neymar ya biya kudin barin Barcelona

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Neymar ya zama dan wasan da aka saya mafi tsada a duniya

Barcelona ta sanar da cewar Neymar ya biya kudin kunshin yarjejeniyar barin kungiyar na fam miliyan 200 da aka sawa duk wata kungiya da take son daukarsa kafin yarjejeniyarsa ta kare.

Ana sa ran Neymar zai saka hannu kan kwantiragi mafi tsada a duniya a Paris St-Germain, bayan da ya nemi bukatar barin Barcelona a ranar Laraba.

Lauyan Neymar ne da kansa ya biya kudin a ofishin Barcelona.

Tun farko mahukuntan La Liga sun ki amince wa kan biyan kudin Neymar da PSG ta bukaci yi domin ya koma kungiyar da wasa.

Hukumar tana ganin ba zai yiwu PSG ta biya kudin Neymar ba tare da take dokokin adalcin ciniki da hukumar Uefa ta kakaba ba.

Labarai masu alaka