Iheanacho ya koma Leicester City

Mancherster City
Image caption Iheanacho shi ne na hudu da ya koma Leicester City

Leicester City ta dauki Kelechi Iheanacho daga Manchester City a kan kudin da ake cewa ya kai fam miliyan 25.

Dan wasan tawagar Najeriya mai shekara 20, ya ci kwallo 21 a karawa 64 da ya buga wa Manchester City, bayan da ya koma kungiyar a shekarar 2015 kan yarjejeniyar shekara biyar.

A bara ne dan kwallon ya tsawaita zamansa a Ettihad zuwa 2021, sai dai an daina sa shi a wasa akai-akai sakamakon komawar da Gabriel Jesus ya yi City a watan Janairu.

Iheanacho ya zama na hadu da Kocin Shakespeare ya dauka don tunkarar kakar bana, da ya hada da mai tsaron raga Eldin Jakupovic, da mai tsaron baya Harry Maguire da mai wasan tsakiya Iborra.

Labarai masu alaka