Waye zai maye gurbin Neymar a Barca?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Aurier ya koma PSG ne a shekarar 2015 daga kungiyar Toulouse

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta tuntubi dan wasan Paris St-Germain (PSG) Serge Aurier yayin da a bangare guda kuma Manchester United ita ma take zawarcinsa, kamar yadda jaridar Manchester Evening News ta bayyana.

Kocin Monaco Leonardo Jardim ya shaida wa Kylian Mbappe cewa kulob din zai sayar da shi kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa, amma ya ce yana jiran wanda zai taya dan wasan ne da kudi mai kauri, in ji Independent.

Jaridar Mirror ta ruwaito cewa Philippe Coutinho ba zai taka wa Liverppol leda ba a wasan sada zumuntar da za su buga da Athletic Bilbao saboda raunin da ya ji. Barcelona tana neman dan wasan don ya maye gurbin Neymar wanda ya koma PSG.

Har ila yau, Barcelona ta raba kafa kan madadin Neymar inda take zawarcin Ousmane Dembele na Borussia Dortmund, in ji jaridar Daily Mail.

Dembele ya ce yana maraba da komawa Barcelona a halin yanzu, kamar yadda Metro ta wallafa.

Cristiano Ronaldo ya amsa cewa yana da muradin komawa Ingila wasa. Dan wasan gaban Madrid din ya bayyana hakan ne yayin da ake sauraren karar da aka shigar kansa game da tuhumar zambar haraji, in ji jaridar Cadena SER.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana tuhumar da zambar haraji a Spain

Kodayake, Madrid tana duba yiwuwar sayar da Gareth Bale ga Manchester United idan za su hada musu da gola David De Gea a cinikin, a cewar jaridar Don Balon ta Spain.

Metro ta ce PSG tana neman dan wasan kungiyar Nice, Jean Michael Seri, kodayake Arsenal tana zawarcin dan wasan.

Monaco ta ce a shirye take ta biya fam miliyan 45 don ta mallaki Alexis Sanchez na Arsenal wanda yake da sauran shekara daya a kulob din, kamar yadda Sun ta wallafa.

Tuttosport ta ruwaito kocin Chelsea Antonio Conte yana cewa zai musanya Andreas Christensen da Antonio Candreva na Inter Milan.

Har ila yau, Chelsea ta musanta cewa Conte yana so ya tilasta wa Diego Costa barin kungiyar, in ji Independent.

Labarai masu alaka