'Madrid ba za ta sayar da Gareth Bale ba'

Bale Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bale ya koma Madrid ne a shekarar 2013 daga Tottenham

Real Madrid ta ba Gareth Bale tabbacin ci gaba da wasa a kungiyar bayan jita-jitar cewa Man U na zawarcinsa, a cewar Observer.

Kungiyar Barcelona tana zawarcin dan wasan Tottenham Dele Alli bayan ta sayar da Neymar a kan fam miliyan 200, kamar yadda Sunday Express ta bayyana.

Hakazalika Bayern Munich tana neman Eric Dier na Tottenham a kan fam miliyan 50, in ji jaridar Sun.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dier mai shekara 23 ya koma Tottenham ne a shekar 2014

Arsenal da Liverpool da Manchester City da kuma Barcelona suna rige-rigen sayen dan wasan Monaco, Thomas Lemar, kamar yadda Sunday Mirror ta wallafa.

Jaridar Sunday People ta ruwaito cewa ne Everton na neman dan wasan Arsenal Danny Welbeck.

Chelsea tana kokarin kasa Liverpool ne yayin da suke ci gaba da zawarcin dan wasan Southampton Virgil van Dijk, kamar yadda Evening Standard ta bayyana.

Labarai masu alaka