Feyenoord ta lashe Dutch Super Cup

Dutch Super Cup Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bayan da kungiyoyin suka tashi kunnen doki, aka yi bugun fenariti

Kungiyar Feyenoord ta ci Dutch Super Cup, bayan da ta yi nasarar doke Vitesse 4-2 a bugun fenariti.

Feyenoord ce ta fara cin kwallo, an kuma yi wa dan wasan Vitesse Karim El Ahmadi keta a da'ira ta 16, amma alkalin wasa Danny Makkaelie bai bayar da bugun ba.

Daga baya Feyenoord ta kara cin kwallo amma Makkelie ya yi amfani da na'urar da take taimakawa alkalin wasa yanke hukunci ya ki amincewa.

Vitesse ta farke ne a bugun fenariti, amma ta yi rashin nasara daga karshe da ci 4-2.