Dambe: Dan Bunza da na Abata Mai babu kisa

Damben gargajiya Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Dogon Bunza da Shagon Abata Mai babu kisa a turmi ukun da suka yi

An dambata tsakanin Dogon Dan Bunza da Shagon Abata Mai a gidan wasa na Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi.

Shagon Abata Mai daga Kudu ne ya bukaci karawa da Dogon Dan Bunza daga Arewa, shi kuwa ya amince suka sa zare.

Wasan nasu ya kayatar matuka, inda suka dunga yin amarya har turmi uku babu wanda yaje kasa, alkalin wasa Turabula ya raba su.

Sauran wasannin da aka yi Shagon Dogon Aleka daga Kudu ya buge Nokiyar Dogon Sani daga Arewa a turmin farko.

Shagon Dogon Aleka daga Kudu a karo na biyu ya buge Bahagon Katsinawa daga Arewa, shi ma a turmin farko ya yi nasara.

Shi kuwa Shagon Turabula daga Kudu doke Shagon Garkuwan Musan Kaduna daga Arewa ya yi a turmin farko.

Wasannin da aka yi babu kisa:

  • Dan Daba Shagon Zakka daga Arewa da Shagon Kato Mai Karfi daga Kudu
  • Shagon Buzu daga Arewa da Shagon Babangida daga Kudu
  • Shagon Isan Jafaru daga Kudu da Shagon Dan Jamilu daga Arewa