Pillars da Plateau United sun raba maki

Kano Pillars
Image caption Har yanzu Plateu United tana ta daya a kan teburin gasar Premier

Kano Pillars da Plateau United sun raba maki daya-daya a tsakaninsu bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 33 a ranar Lahadi.

Plateau United ce ta fara cin kwallo ta hannun Ibeh Johnson a minti na 17 da fara tamaula, kuma Pillars ta farke ta hannun Hamza Abba Tiya, bayan da aka dawo daga hutu.

Ga wasu sakamakon wasannin mako na 33 da aka yi:

  • ABS 2-0 Remo
  • 3SC 2-1 Gombe
  • Tornadoes 1-0 El-Kanemi
  • FCIU 1-0 Nasarawa
  • MFM 0-0 Enyimba
  • Lobi 2-4 Abia Warriors
  • Wikki 1-1 Rangers
  • Sunshine 1-0 Akwa United