Wenger na fatan nasararsu a kan Chelsea ta bude musu hanya a Premier

Arsene Wenger da 'yan wasansa rike da Community Shield Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsene Wenger na fatan nasarar ta zamar musu mabudin sa'a a Premier

Arsene Wenger ya ce yana fatan kungiyarsa za ta samu kwarin guiwa daga nasarar da ta yi a wasan da suka doke Chelsea suka dauki Community Shield, ta kauce wa sake fara gasar Premier ta bana da bacin-rana, a wasan da za su yi da Leicester ranar Juma'a.

Gunners din dai suna shan kashi ne a dukkanin wasansu na farko na Premier da suka yi a uku daga cikin kaka hudun da ta wuce.

Za su kara da Leicester a wasan nasu na farko ne na bana a filinsu na Emirates, bayan nasarar da suka samu a kan Chelsea, da bugun fanareti, bayan sun tashi kunnen doki 1-1.

Wenger ya ce, ''kamata ya yi mu yi kokari mu shiga gasar Premier da irin kwazo da kishin yanzu, sannan mu ga inda za mu kai.''

Makomar kociyan ta kankane duk wasu al'amura a kungiyar a kakar da ta wuce, amma bayan da ya sabunta kwantiragin sa da shekara biyu a watan Mayu, yanzu kuma hankali ya koma kan makomar 'yan wasansa biyu.

Alexis Sanchez da Mesut Ozil sun shiga shekarar karshe ta kwantiraginsu, kuma dukkaninsu ba sa cikin tawagar da ta doke Chelsea, ko da yake sun halarci murnar karbar kyautar gasar bayan fanaretin da Olivier Giroud ya ci.

Labarai masu alaka